By Ishaq Dabai
Matsakaicin farashin da masu amfani da shi suka biya na Kananzur na Ƙasa (NHK) ya faɗi zuwa Naira 400.01 akan kowace lita a wannan makon.
Wannan yana nuna raguwar kashi 7.9 cikin ɗari idan aka kwatanta da naira 434.39 a kowace lita da aka rubuta a ƙarshen Satumba na wannan shekarar.sannan, farashin da masu amfani da man Gas ke biya akan kowace lita na Man Gas (dizal) ya faɗi da kashi 0.16 cikin ɗari a wannan makon zuwa Naira 254.21 daga Naira 254.64 zuwa watan Satumba na ƙarshen shekarar 2021.
Dangane da bayanai da kamfanin globalpetrolprices.com, ya zuwa wannan makon farashin galan kananzir ya tsaya akan Naira 1,514.20 yayin da farashin galan din Diesel ya tsaya akan Naira 962.29.
Idan aka kwatanta da bayanai daga Ofishin Ƙididdiga na Ƙasa (NBS) NKH da Diesel a cikin lokacin watan Satumba, farashin da aka biya a galan NKH ya faɗi da kashi 1.73.
Rahoton NBS na watan Satumba ya bayyana cewa: “Matsakaicin farashin lita da masu amfani da shi ke bayarwa na na cikin Gida na Ƙasa ya ƙaru da kashi 8.6 cikin ɗari a kowane wata (MoM) da kashi 24.8 bisa ɗari na shekara (YoY) zuwa Naira 434.39 a watan Satumba na shekarar 2021 daga Naira 400.01 a watan Agusta na shekarar 2021.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa matsakaicin farashin galan da masu amfani da shi suke biya na Kananzur na Ƙasa ya ƙaru da kashi 16.25 cikin ɗari na MoM da 25.3 YoY zuwa naira 1, 540.82 a watan Satumba 2021 daga naira 1, 325.39 a watan Agusta shekarar da muke ciki ta 2021.
“Jihohin da aka fi samun matsakaicin farashin galan na kananzir sune Abuja ana sayar dashi akan (naira 2, 766.67), Bauchi (Naira 1, 981.54) da Adamawa akan (Naira 1,975.00) sai jihar Imo (Naira 1991.23) da kuma Yobe akan (Naira 1,080.00). ”
A kan dizal, NBS ta ce: “Matsakaicin farashin da masu amfani da shi suka biya na Man Gas (dizal) ya karu da kashi 0.17 cikin dari na MoM da kashi 15.9 na YoY zuwa Naira 254.64 a watan Satumba 2021 daga Naira 254.21 a watan Agusta 2021.”