By Ishaq Dabai
An gurfanar da wata mata mai shekaru 42, Ganiyu Aniyat, a gaban Kotun Majistare dake Osogbo kan zargin zambar kudi Naira miliyan daya.
Aniyat, wanda ba a bayyana wurin da take zaune ba, ta musan ta aikata laifuka biyu na zamba da kuma sata da ake tuhumarta dasu.
Dan sanda mai gabatar da kara, ASP John Idoko, ya shaidawa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifukan a wani lokaci a cikin a shekarar 2018 a cikin garin Osogbo.
Idoko yace Aniyat ta damfari Mista Tayo Oduntan akan kudi naira miliyan daya bayan data kasa ba shi adadin kudin da aka amince da shi.inda Yace laifin ya ci karo da sashi na 419 da 390 na kundin laifuka 34, 11, na Dokokin jihar Osun na shekarar 2002.
Lauyan dake kare wanda ake kara, Mista Oladipupo Olatunbosun, ya roki kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa cikin sharuddan masu sassaucin.
Mai shari’ar kotun Majistare, A. Adeyewa, ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi Naira 400,000 tare da mutum daya da zai tsaya mata.
Adeyewa yace wadanda zasu tsaya mata dole ne su kasance a cikin hurumin kotun, su bayar da shaidar biyan haraji, sannan su mika kwafin hotunan fasfot din su da takardar shaida ga magatakardar kotun.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa alkalin kotun ya daga cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba don ci gaba da sauraro.