Babban Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, Mohammed Adamu a ranar Alhamis ya bayyana cewa; tuni suka kammala shirya jami’ai na musamman domin tura su yankin kudu maso yammacin Nijeriya domin magance matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Sufeto Adamu ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da manema labarai lokacin da ya kai ziyara hedikwatar ‘yan Sandan dake garin Akure a wani mataki na dakile matsalar tsaro a yankin. Sufeto Janar Adamu ya ce ya gana da wadannan jami’ai na musamman da kuma gwamnoni da Sarakunan gargajiya a yankin a wani taro da ‘yan sandan suka shirya a garin Ibadan a ranar Litinin.