By Abbas Yakubu Yaura
Bankin Duniya ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 9.4 za su iya zama bakin haure a Najeriya nan da shekarar 2050. Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wani sabon rahoton bankin duniya,kan Yanayi Hijira a Kasashen Yammacin Afirka.
Rahoton ya bayyana cewa ba za a iya kaucewa ƙaura daga cikin gida ba amma illar ta bambanta daga wannan ƙasa zuwa waccan saboda yadda yanayin hulɗa da al’amuran al’umma da zamantakewa da tattalin arziki a matakin gida.
“Babu wata kasa a yammacin Afirka dake da kariya daga yanayin ƙauran a cikin gida, amma girman kowace ƙasa zai dogara ne akan yadda yanayin hulɗa da al’amuran al’umma da zamantakewa da tattalin arziki a matakin gida.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Rahoton ya bayyana cewa: “An yi hasashen kasashen Nijar da Najeriya da Senegal za su kasance kan gaba a yawan ‘yan ci-rani a cikin gida nan da shekarar 2050:inda za su kai miliyan 19.1, zuwa miliyan 9.4, da miliyan 1.0, bi da bi, a cikin mummunan yanayi,” in ji rahoton.
Sannan Rahoton ya bayyana cewa za a samu wani yanayi mai cike da kyama kan yanayin da ake da shi, inda Najeriya ke da matsakaicin yawan bakin haure na cikin gida na mutane miliyan 8.3 nan da shekarar 2050.
Kazalika Rahoton ya kara da cewa, “Daga cikin kasashen yammacin Afirka dake gabar teku, ana hasashen Najeriya za ta fi kowace kasa yawan bakin haure a cikin gida a karkashin yanayi mara kyau nan da shekarar 2050 (miliyan 8.3) inda zata zarce Senegal da (miliyan 0.6) ita kuma ta zarce Ghana (0.3).
“Duk da haka, ƙananan ƙasashe, irin su Benin, suma suna nuna alkaluman ƙaura na cikin gida a matsayin kaso 1.62 na al’ummar Benin idan aka kwatanta da kashi 1.93 na Najeriya sannan kuma Senegal ta samu kaso mafi girma da kashi 1.98 cikin ɗari). ”
A cewar rahoton, yanayin gudun hijira zai fi faruwa a yankin Sahel kamar arewacin Najeriya.Rahoton ya ci gaba da cewa jihohin da abin ya shafa a arewacin Najeriya sun hada da Kano, Katsina, da Sokoto, wadanda ke fama da matsalar talauci.
Comments 1