Mafiya yawa daga cikin Al’ummar karamar hukumar Okitipupa dake jihar Ondo, sun yanke shawarar ci-gaba da amfani da Itace da kuma Gawayi wajen Girki.
Sun yanke wannan shawara ne bayan da sinadarin Gas da ake girki da shi yayi tashin Gwauron zabi lamarin da ya sanya tsakanin Gas da Talaka sai dai kallo.
Karuwar farashin Gas din baya rasa nasaba da yadda ake cigaba da fama da karancin sa a duniya, kuma tuni kasashe da dama suka yanke shawarar komawa amfani da Gawayin.
Yanzu dai farashin Gas ya tashi daga Naira 400 kan kowane Kilogram daya, zuwa Naira 650 da 700, maimakon hakan yanzu Naira 100 zuwa 200 zata isa mutum ya siyi Itace ko Gawayi domin girki da shi.