Wani mai rajin kare yancin kabilar Fulani Ab Sow ya kalubalanci mamallakin kamfanin Facebook Mark Zuckerberg bisa sauya sunan kamfanin daga Facebook zuwa Meta.
Cikin wata wasika da Bafulatanin ya aikewa da Mark ya bayyana cewa kalmar ”Meta” kalma ce ta fulatanci, kuma yayin da ya tashi amfani da kalmar bai nemi shawarar su ba domin amfani da kalmar.
Sakamakon hakan Sow ya ce dole ne sai dai mai kamfanin ya dinga baiwa Kungiyar Fulani kaso 20 cikin 100 na duk ribar da yake samu a shekara sakamakon amfani da kalmar su.
Ya kara da cewa idan har mai kamfanin Facebook din ya gaza basu wannan kason, to kuwa zasu dauki mataki na Shari’a akansa.
Ab Sow ya Bayyana ma’anar ”Meta” da Yaren fulatanci da cewa tana nufin ”Maimaici”.