Hukumar zabe mai zaman kanta ta Ƙasa INEC ta ce daga cikin cibiyoyin kada kuri’a 5, 720 da ake da su a jihar Anambra 86 har yanzu babu masu kada kuri’a, dai dai lokacin da ya rage sati guda kafin gudanar da zaben gwamnan a jihar.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya sanar da hakan a yau, yayin wani taro da hukumar ta gudanar da wasu daga cikin wakilan Jam’iyyun a Abuja.
A don haka ne hukumar ta INEC ta bayyana jam’iyyun cewa ba za ta aike da kayayyakin zabe zuwa ga cibiyoyin da babu masu zabe ba a jihar.
Ya kuma ce cibiyoyi 894 wadanda ke daukan kaso 15.6 cikin dari na jihar, suna da masu zabe ne daga 1 zuwa 49.