Daga: Abbas Yakubu Yaura
A ranar Alhamis din data gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Ahun dake Oro Ago a karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara inda suka yi awon gaba da shanu 15 bayan sun farwa wani Bafulatani makiyaya mai suna Muhammadu Bello, inda suka bar shi a sume.
Makiyayan da suka ji rauni an ceto, kuma kungiyar ‘yan banga ta Miyetti Allah dake yankin takai su sashin ‘yan sanda na Oro Ago.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, kakakin hukumar NSCDC na jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, yace, “Mai kiwon shanun ya samu munanan raunuka, kuma ya kusa rasa ransa bayan daya sume sakamakon illar da akayi masa a kansa.An kai shi asibiti domin samun kulawar da ta dace ta likitoci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa rikicin Makiyaya da manoma bawani sabon al’amari bane inda ya zama ruwan dare a wasu sassan najeriya duk da kokarin da mahukunta sukeyi naganin an kawo karshen wannan ta kaddama.