Daga: Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 8 ne suka mutu yayin da 46 suka jikkata a gobara 140 data tashi a jihar Kaduna tsakanin watan Yuni da Oktoba, kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Mista Paul Aboi, wanda ya bayyana hakan ga jaridar Dimokuradiyya a ranar Alhamis, yace an ceto mutane 17 daga cikin lamarin.
A cewarsa, an samu rahoton mutuwar mutane shida a cikin 57 na tashin gobarar a watan Yuli da Agusta da suka gabata.
Sannan “An ceto kadarorin kimanin na Naira biliyan 1.1 daga barna tashin gobarar a cikin wannan lokaci, yayin da tashin gobarar ya lalata dukiyoyin da takai Naira biliyan 2.4,” inji shi.
Mista Aboi ya ci gaba da cewa gobarar 140 ta barke a Kaduna, Zariya da Kafanchan, inda yace hukumar na yin iyakacin kokarinta wajen ganin an rage afkuwar lamarin ta hanyar wayar da kan jama’a kan matakan kare kai daga gobara.
Kazalika Ya dora alhakin barkewar tashin gobarar a kan sakaci da shigar da na’urorin wutar lantarki da bai dace ba, yana mai jaddada cewa ya kamata mazauna yankin su yi taka-tsan-tsan wajen sarrafa na’urorin lantarki a cikin gidajen su.