By Abbas Yakubu Yaura
An kashe biyu daga cikin masu ibada 66 da aka sace a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba a cocin Emmanuel Baptist dake Kakau Daji, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Rabaran Joseph John Hayab, shugaban kungiyar ta CAN reshen kaduna, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Lahadi.
Sannan yace ‘yan bindigar sun bude wuta a kan biyar daga cikin wadanda suka mutu a ranar Asabar, inda suka kashe biyu yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka kuma a halin yanzu suna kwance a asibiti.
“Rayuwar masu ibadar Kaduna da aka sace na cikin hadari kuma suna bukatar gwamnati da jami’an tsaro shiga lamarin cikin gaggawa.
“Rashin tsaro a jihar Kaduna ya ci gaba da karuwa fiye da tunaninmu kuma yana barazana ga zaman lafiyar al’umma.
“Kungiyar CAN tana kira ga daidaikun mutane, kungiyoyi, masu rike da madafun iko, musamman gwamnatin tarayya da sauran kasashen duniya dasu kawo mana dauki, “Mugunta da muke fuskanta ya fi abin da talakan Kaduna da Najeriya zai iya dauka.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa kungiyar ta “CAN tace tana kira ga daukacin kiristoci da al’ummar jihar kaduna dasu hada kai wajen yakar wannan muguwar dabi’a da kuma sanya ido,” inji shi.