Hukumar hada-hadar hannayen jari ta kasa (SEC) ta kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a a kauyukan jihar Gombe domin wayar da kan mata da matasa muhimmancin saka hannun jari a kasuwar Najeriya.
An gudanar da gangamin wayar da kan jama’an ne a kananan hukumomin Akko, Billiri, Dukku, Kaltungo da Yamaltu/Deba a jihar Gombe.
Shirin hada kudin, wani shiri ne na Babban Bankin Najeriya (CBN) da SEC don inganta hanyoyin samun kayayyaki da ayyuka na kudi.
Da yake jawabi a garin Dukku, na karamar hukumar Dukku, Mista Tunde Isaac na Sashen Kula da Zuba Jari na kasa SEC, ya ce yawaitar tsare-tsaren Ponzi ya sa ya zama wajibi SEC ta wayar da kan jama’a, musamman wadanda ke yankunan karkara, kan illolin da ke tattare da baiwa masu damfara kudade.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nigeria Da Nijar Sun Gana Kan Magance Rikicin Boko Haram
“Saboda yawan tsare-tsaren Ponzi a kasuwa, mutane za su zo wurin wadannan mutane su yaudare su, don su zuba jarin N10,000 su samu N20,000 cikin kankanin lokaci,” inji Isaac.
Comments 1