Manoma a wuro Joi dake Kwami ta Gabas a ƙaramar hukumar Kwami ta Jahar Gombe sun koka akan rashin da suka yi, biyo bayan cin iyaka da Makiyaya suka yi a gonakin su.
Gwamnatin Jahar a ƴan kwanakin nan bayan ta gudanar da taron tsaro ta tattauna akan abubuwa da dama, inda ta gargaɗi Manoma dasu guji bada dama da za’ayi kiwo, a yayinda ta sanar da watan Janairu a matsayin lokacin da za’a cire amfanin gonar.
Gwamnatin ta kuma hana hijirar da makiyaya suke yi daga wasu jahohi har ƙarshen cire amfanin gona.
KARANTA WANNAN LABARIN: ZAƁEN 2023: Wasu Malamai Da Ƴan Siyasa A Kano Sun Nuna Goyon Bayan su Ga Yahaya Bello
Dayake tabbatar da lalata masu amfanin gonar, Dagacin Ƙauyen Wuro Joi Babayo Abubakar yayi nuni dacewar lalata amfanin gonar yana haifar da tsaiko akan abinci, yana mai jaddada cewa wanda lamarin ya shafa a biyasu diyya.
Majiya ta nuna cewa amfanin da aka lalata sun ƙunshi Wake, Dawa, wanda aka ƙiyasta zasu kai miliyoyin Nairori.
“Gonakin mu da muka noma wake da dawa makiyaya sun lalata su da shanin su, anan Wuro Joi, muna neman tallafin gwamnati, mun zuba kuɗi da yawa domin wannan amfanin,” inji Abubakar.