An yi ta murna a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno bayan da sojojin Najeriya suka dakile wani hari da aka kai da sanyin safiyar yau Juma’a.
Jaridar Dimukuradiyya ta ruwaito yadda sojoji suka fatattaki mayakan Boko Haram daga garin.
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun mamaye garin ne da misalin karfe 6:35 na safe, inda suka rika harbi ta ko’ina.
Hakan dai ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna garin sai dai rahotanni sun ce sojoji sun yi ta harbe-harbe, lamarin da ya tilasta musu ja da baya.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa maharan ba su iya tsayawa har na tsawon mintuna 30 ba.
“Zan iya tabbatar muku da cewa mayakan Boko Haram sun yi wani yunkurin da safiyar yau amma hakan bai yi nasara ba, sojojin da ke cikin garin Damboa sun dakile shi nan take,” in ji majiyar.
Wani ma’aikacin Civilian Joint Task Force, ya shaida wa jaridar Daily trust cewa wasu mutanen yankin sun samu raunuka a harbin bindiga a garin Kala, wani kauye da ke kusa da garin Damboa.
“Akalla mutane 8 ne suka samu raunukan harbin bindiga a kauyen Kala dake kusa da garin Damboa.”
Majiyar ta ce “Sojojin sun yi babban aiki kuma kamar yadda muke magana yanzu, an yi murna a Damboa.”