Majalisar dokokin Imo ta yi kira ga gwamna Hope Uzodinma da ya gaggauta shiga tsakani kan zaizayar kasa da ta addabi sassan karamar hukumar Ikeduru ta jihar.
Majalisar ta yi wannan roko ne biyo bayan wani kudiri da wakilin Ikeduru, Uche Ogbuagu na jam’iyyar (APC), ya gabatar a zamanta na ranar Alhamis a Owerri.
Da yake gabatar da kudirin, Mista Ogbuagu ya ce Okwu, Owu Amakohia, Amalla, da Avuvu da ke mazabar sun lalace sakamakon zaizayar kasa da zabtarewar kasa.
Ya kara da cewa yankin ya yi asarar kayayyakin tattalin arziki, filayen noma, makarantu, da kuma hanyoyin kuma a bi wajen kawar da zaizayar kasa.
Dan majalisar ya ce lamarin ya sa mutanen yankin sun zama ‘yan gudun hijira. Ya kuma roki gwamnan da ya umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta dauki “matakin gaggawa” a kan matsalar.
Ya kuma yi kira ga gwamnan da ya hada kai da hukumar kula da zaizayar kasa da ruwan sha ta Najeriya (NEWMAP) domin magance matsalar ta dindindin.
Da yake goyon bayan kudirin, Arthur Egwim (APC/Ideato North), ya ce mazabarsa ma tana fuskantar irin wannan matsala, kuma ya yi kira da a saka yankinsa cikin ayyukan da za a yi. Sai ya yi kira da a gayyaci ko’odinatan hukumar NEWMAP na Jiha domin sanar da Majalisar game da ayyukan su a jihar.
Uju Onwudiwe (APC/ Njaba), a nata gudunmawar, ta ce NEWMAP ta kasa gudanar da ayyukanta a jihar. Ta yi kira da a sake gina hanyoyin cikin gaggawa, “ba wai wasu matakan kwantar da hankali ba.”
Shugaban Majalisar, Kennedy Ibe (APC/Obowo), ya yanke hukuncin amincewa da kudirin. Tare da umurmartar magatakarda, Chinelo Emeghara, da ya gayyaci SEMA, NEWMAP da sauran masu ruwa da tsaki don “jin ba’asi” ga majalisar a ranar 23 ga Nuwamba.