A ranar Larabar da ta gabata ce gwamnonin Arewa maso Yammacin kasar nan suka kai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas ziyarar ta’aziyya kan ginin bene mai hawa 21 da ya ruguje a kan titin Gerrard, Ikoyi wanda ya hallaka mutane 45 a ranar 1 ga Nuwamba.
Kungiyar gwamnonin arewa maso yamma da shugabanta kuma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da takwaransa na Kano, Dr Abdullahi Ganduje, suka wakilta, sun jajanta wa al’ummar Legas da iyalan wadanda suka rasu a wannan mummunan lamari.
Sun yabawa Sanwo-Olu da ya kafa kwamitin bincike don warware matsalolin da suka dabaibaye ginin da ya ruguje.
Da yake jawabi a ziyarar da ya kai ginin da ya ruguje, Gwamana Masari ya ce, “Muna nan muna wakiltar gwamnonin Arewa-maso-Yamma don mu yi ta’aziyya ga Gwamna Sanwo-Olu, da iyalan mamacin da daukacin al’ummar Legas kan wannan mummunan lamari da ya faru. ”
Da yake bayyana cewa ba za a iya guje wa manyan gine-gine a jihar Legas ba, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa irin wadannan gine-gine ba za su yi asarar rayuka da dukiyoyin jama’a ba.
Shima da yake jawabi, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa Sanwo-Olu bisa daukar matakin gaggawa na nuna damuwa a lokacin da ginin ya ruguje.
Ya ce, “Lagos babban birni ne. Idan aka kwatanta shi da sauran manyan biranen duniya da kuma la’akari da halin da Legas ke ciki saboda rashin isassun filayen raya kasa, karuwar yawan jama’a, batun gina manyan bene ya zama tilas kuma ba za a iya kauce masa ba amma abin takaici ne muka tsinci kanmu a ciki Saboda abin da ya faru.”
Da yake mayar da martani, Sanwo-Olu ya yabawa gwamnonin bisa jajantawa gwamnati da jama’ar jihar Legas kan ginin Ikoyi da ya ruguje.