Kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan jama’a da tantance ‘yan kasa ya bayyana cewa sama da Naira biliyan 190 aka ware domin gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2022.
Shugaban kwamatin, Sanata Sahabi Alhaji Yaú ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kare kasafin kudin 2022 na hukumomin da ke karkashin kulawar kwamitin sa a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar.
Sanata Ya’u ya ce: “Sama da Naira biliyan 190 an yi kasafin kudin aikin. Muna jiran shugaban kasa ya bayyana lokacin da ayyukan za su fara.”
Game da cewa 2022 shekara ce kafin zaɓe, Yau ya ce: “Sun yi tunanin lokaci ne mafi kyau. Tabbas sun yi lissafinsu kuma shugaban kasa a shirye yake ya gudanar da kidayar jama’a nan da shekarar 2022.”