By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 8,730 ne a jihar Jigawa suka ci gajiyar aikin jinya na ido kyauta da Majalisar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) ta yi.
Gwamnatin jihar Jigawa ta tallafa wajen bada goyan baya tare da wayar da kan jama’ar jihar.
Kungiyar WAMY tare da hadin gwiwar gidauniyar Mallam Inuwa, sun kuma bayar da tallafin gilashin magani ga majinyata a yayin gudanar da taron na kwanaki hudu da aka kammala a ranar Laraba.
Shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar, Ahmed Inuwa, yace atisayen zai taimaka matuka wajen rage nauyi da yaduwar makanta da cututtukan ido a cikin al’umma.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da maza da mata da kananan yara daga kananan hukumomin jihar.
Kazalika Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “An yi wa marasa lafiya 637 aikin tiyata kyauta, inda Marasa lafiya 500 suka sami gilashin idanu mai dauke da magani. An bayar da magunguna ga majinyata 7,593,” a cewar Inuwa.
Shugaban kwamitin gudanarwa, Yusuf Hussaini Baban, ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin Qatar bisa daukar nauyin aikin jinyar.
“Muna godiya ga kyawawan halayen jagoranci da mutanen Qatar wadanda ke ba da kudade da kayan aiki da ke taimakawa bil’adama da inganta zaman lafiya a fadin duniya,” in ji shi.
Kazalika yace “Za mu ci gaba da hada kai ga irin wadannan kungiyoyin agaji wajen neman rahamar Allah Ta’ala ta hanyar taimaka wa masu fama da matsalar ido da sauran matsalolin lafiya.”