Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta fara aikin sake duba hukumar gano tsiyayar mai ta kasa (NOSDRA) domin ta fuskanci hukunci mai tsauri kan kamfanonin mai da ke da hannu a zubar da mai a kasar.
Ministar Muhalli, Sharon Ikeazor wadda ta bayyana hakan a ranar Alhamis a wajen taron mako-mako na ministocin da aka yi a fadar gwamnati, ta bayyana cewa, an samar da kwakkwaran tsarin shari’a don dakatar da malalar man da ake cigaba da yi a wannan lokaci.
Ministan Muhalli ta kuma bayyana cewa an shawo kan matsalar malalar mai ta OML29 a garin Nembe, da ke jihar Bayelsa, yayin da ta dora alhakin zubar da man da al’ummar yankin ke yi.
A cewarta, an tura ma’aikata da kayan aikin da suka dace domin fara aikin farfaɗowa da gyare-gyaren da NOSDRA ke gudanarwa, domin hukumar ta ba da tabbacin cewa za a kammala tantance illar da matsalar ta shafa nan da wata guda.
Bugu da kari, Ikeazor ta nuna cewa gwamnati na kokarin samar da wasu hanyoyin rayuwa ga al’ummomin yankin domin dakile ayyukan da ba su dace ba, wadanda ke haifar da zagon kasa ga man.
Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan mace-mace sakamakon hayaki a duniya, inda akasari mata ne a cewar ma’aikatar muhallin.
Gwamnati na fatan sake dawo da dafaffen abinci mai tsafta da shirin samar da iskar gas (LPG) wanda aka bayyana a matsayin na asali, don ba da damar rahe mace-mace tare da kare rayayyun da ke kasar.