Gabanin zaben shekarar 2023, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce shirin jam’iyyar APC mai mulki shi ne za ta yi nasara a zaben.
Gwamna Sule, wanda ya kasance bako a shirin Siyasar Gidan Talabijin na Channels A ranar Laraba, ya ce jam’iyyar na taka-tsan-tsan wajen gudanar da taronta da kuma zabar manyan jami’an da za su gudanar da harkokinta.
“Shirin mu ba shine mu fadu zabe a 2023 ba kuma duk abun da muke yi kenan,” in ji gwamnan Nasarawa.
“Don haka ne muke yin taka-tsan-tsan a majalisa, muna yin taka-tsan-tsan wajen zabar jami’an a matakin kasa, muna taka-tsan-tsan wajen yanke hukunci.
“Maimakon tsoratarwa, abun da ya kamata duk wanda ke son wannan mulki to ya gabatar da kansa a matsayin mutam mai gaskiya, ƙwararrun mutane waɗanda ke da ikon karbar mulki daga hannun Muhammadu Buhari tare karasa gina abun da ya fara.”
Gwamnan ya kuma yi magana game da rade-radin da ake ta yadawa na aniyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da dai sauransu.
Yayin da yake bayyana cewa masu neman shugabancin kasar nan sai sun bunkasa tinanin su shugabanci domin gadar shugaba Buhari a 2023, Gwamna Sule ya ci gaba da cewa dole ne su tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa suna da dukkan abun da ya kamata wajen jagorantar kasar.
A cewarsa, ‘yan Najeriya ne za su tantance wanda zai gaji Buhari a zaben. “Kowane daya daga cikinsu na iya shigowa ya iya nunawa jama’a da kuma nuna goyon baya. A karshen wannan rana, ‘yan Najeriya ne ke da ikon yin hakan (zabar),” in ji shi.
Ya kara da cewa “Da zarar kun sami damar gamsar da ‘yan Najeriya cewa wannan shi ne abun da ya dace, mutane suna da damar kwatanta su da fitar da wanda shi ne mutumin da ya dace,” in ji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Duk da cewa har yanzu ba a tantance takamaiman ranar ba, amma kwanan baya shugaba Buhari ya amince da watan Faburairun 2022 ga jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta na kasa.