By Abbas Yakubu yaura
A ranar Juma’ar ne gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarnin rufe kwalejin Dowen dake Lekki, biyo bayan binciken mutuwar dalibin makarantar Sylvester Oromoni.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Legas, Ganiu Lawal.
Sanarwar tace, “Gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarnin rufe kwalejin Dowen dake Lekki har sai an kammala bincike kan mutuwar dalibin makarantar Sylvester Oromoni Jnr.
“Kwamishiniyar ilimi Misis Folasade Adefisayo ce ta sanar da rufe makarantar bayan wata ganawa da jami’an gudanarwa na ma’aikatan makarantar.
“Kwamishiniyar ta yi kira da a kwantar da hankula, tana mai cewa ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen gano tushen lamarin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Mutuwar dalibar kwalejin, Oromoni Jnr, mai shekaru 12, ta haifar da martani daban-daban daga mashahuran mutane da ‘yan Najeriya baki daya.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan uwan daliban sun ci zarafin Oromoni tare da lakada masa duka.inda da ake kyautata zaton ya samu rauni ne ya kai ga mutuwarsa, a cewar wani ma’abocin Twitter mai rike da hannu @perrisonoromoni, wanda ya yi ikirarin cewa shi dan uwan yaron ne.
Sai dai a wata sanarwa data fitar a ranar Larabar data gabata, makarantar ta musanta dukkan zarge-zargen dake nuna cewa ba a zalunce shi Oromoni ba, kuma ba a yi masa dukan tsiya ba, sai dai kawai ta yi korafin ciwon kugu bayan buga kwallon kafa.
Mahaifin yaron, mai suna daya da dalibin, ya bayyana cewa sabanin yadda kwalejin Dowen ta fada a cikin sanarwar, abokin dangin da suka aika ya dauko Oromoni Jnr. daga makarantar ya bayyana yanayi na daban-daban.
A halin da ake ciki, Kwalejin Dowen, a cikin sakon imel data aika wa iyaye da sanyin safiyar Juma’a, ta bayyana cewa kada dalibai su zo makaranta a ranakun Juma’a, 3 ga watan Disamba da Litinin, 6 ga Disamba, saboda faruwar lamarin.