By Abbas Yakubu yaura
Wata kotun majistare dake Kaduna a ranar Juma’a ta yanke wa wani matashi dan shekara 26 mai suna Garba Hassan hukuncin daurin watanni hudu a gidan yari bisa samunsa da laifin sace kayan mata dana yara kanana da kudinsa ya kai Naira 90,000.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hassan wanda ke zaune a Kawo ta jihar Kaduna, an yanke masa hukuncin ne bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na aikata laifuka da kuma sata.sai dai kuma ya roki kotun data yi masa sassauci kan hukuncin da zata yanke masa.
Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya gargadi mai laifin daya daina aikata laifuka a nan gaba sannan ya ba shi zabin biyan tarar naira 5,000.
Tun da farko, mai gabatar da kara, Insifecta Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wani James Raphael na Malali ya kai karar sa ofishin ‘yan sanda na Gabasawa a ranar 25 ga watan Nuwamba.
Leo yace wanda ake tuhuma da laifin shiga shagon mai karar dake kan titin Ahmadu Bello Way ya kwashe kayan sa na mata da na yara, wanda kudin sa ya kai naira 90,000.
Mai gabatar da kara yace wani mai gadi ne ya kama wanda ake tuhuma a kusa da ginin a lokacin da yake kokarin tserewa da kayan daya sace.
Leo yace yayin binciken ‘yan sanda, Hassan ya amsa laifin satar kayan.Ya yi nuni da cewa laifukan sun ci karo da sashe na 234 da 59 na dokar hukunta manyan laifuka ta jihar Kaduna ta shekarar 2017.