By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaron ruwa sun cafke wani jirgin ruwa mai suna MT TIS IV tare da kama wasu mutane 20 da ake zargin barayin danyen mai ne a garin Akassa dake karamar hukumar Brass a jihar Bayelsa.
Kwamandan, NNS Soroh, Commodore Patrick Effah, shine wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin a Yenagoa, babban birnin jihar, cewa dukkan wadanda ake zargin ‘yan Najeriya ne.
Sannan yace bayan kama jirgin, an gano cewa jirgin yana dauke da kusan lita 700,000 (kimanin metric ton 603 ko ganga 4,402) na danyen mai da aka samu ba bisa ka’ida ba wanda ya kai kimanin dalar Amurka 315,500 dai dai da (Naira miliyan 148) ba tare da amincewar bukatar haka ba.