By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Litinin, ya gana da shugaban kasar jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, a wani bangare na kokarin kawo karshen duk wani nau’in ‘yan fashi da makami a Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Sakataren yada labarai na gwamnan, Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, yace shugabannin biyu sun gana ne a fadar shugaban kasa dake Yamai.
Taron dai an yi shi ne domin tattauna batutuwan da suka shafi tabarbarewar tsaro musamman a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da jamhuriyar Nijar tare da kuduri aniyar binciko wasu fannonin tallafi da hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Nijar da jihar Zamfara.
Gwamna Matawalle ya yi wa shugaba Bazoum bayanin irin matakan da gwamnatinsa ta dauka na kawo karshen duk wani nau’i na miyagun laifuka a yankin.
Gwamnan yace baya ga shirin zaman lafiya da sulhu daya kaddamar, gwamnatinsa ta baiwa jami’an tsaro bayanan sirri kan yadda za a iya gano masu ba da labari ga ‘yan fashi da makami da kuma abokan huldar su.
Sannan ya bukaci a yi taro akai-akai kan harkokin tsaro da Ministan Tsaro na Nijar da Gwamnan Maradi da Gwamnan Jihar Zamfara da na Jihohin Katsina da Sokoto domin kawo karshen matsalolin tsaro da kasashen biyu ke fuskanta.
Da yake mayar da martani, Shugaba Bazoum ya gode wa Gwamna Bello Matawalle bisa wannan ziyarar da kuma duk wani kokari da ya yi na kawo karshen matsalolin rashin tsaro dake addabar kasashen biyu, musamman ma kan iyakar Maradi da Arewa maso Yammacin Najeriya.
Shugaban kasa Mohamed Bazoum ya bukaci Matawalle daya ci gaba da kokarin daya ke yi na magance matsalar rashin tsaro a Zamfara ta hanyar samar da sabbin hanyoyin samar da zaman lafiya da aka riga aka samu a yankin, yana mai cewa gwamnatin Jamhuriyar Nijar a shirye take ta ba da goyon baya a yaki da rashin tsaro yankin.
Shugaba Bazoum ya kuma bukaci gwamnonin Najeriya dasu aiwatar da dokar hana shigo da babura baki daya zuwa Najeriya.
Shugaban ya yi nuni da cewa matsalar ‘yan fashi da makami a fadin jamhuriyar Nijar na zuwa ne daga Madawa da Bayan Dutsi har zuwa Najeriya ta yankin Maradi, amma ya yi fatan da taron da kuma goyon bayan da Gwamna Matawalle ya baiwa gwamnatin Nijar, lamarin zai kasance zama abu na baya.