By Abbas Yakubu Yaura
Wani manomi mai suna Landan Omoru da aka yi garkuwa da shi a wasu gonaki a yankin Agric dake Esa Oke a jihar Osun, ya samu ‘yanci.
An bayyana cewa, Omoru, wanda ake zargin makiyaya ne suka yi garkuwa da shi tare da matarsa, Blessing, a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, 2021, an sake shi a ranar Juma’ar data gabata a garin Aramoko, jihar Ekiti.
Masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa kuma sun bukaci a biya su naira miliyan 37.
Wata majiya mai karfi da jami’an tsaro data nemi a sakaya sunanta a ranar Litinin ta shaida wa wakilinmu cewa an biya kudin da ba a bayyana adadinsu ba a matsayin kudin fansa kafin a sako Omoru.
An kuma bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun tattara tarin sigari da abubuwan sha kafin a sako wanda abin ya shafa a Aramoko, yayin da tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da mafarautan yankin suka shiga dajin suka kubutar da shi.
Idan dai ba a manta ba a baya jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an kubutar da matar manomin a garin Ijebu-Jesa dake jihar Osun bayan da tawagar jami’an tsaro dake aikin ceto suka matsa lamba ga masu garkuwa dasu.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, “Amma kafin a sako mijin an biya kudin fansa. Ban san adadin da aka biya ba. An sako mutumin ne a Aramoko dake jihar Ekiti a ranar Juma’ar data gabata.
Koda aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, yace ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun kubutar da wanda lamarin ya shafa, lokacin da suka matsa lamba kan masu garkuwa da su.
Sai dai kuma da aka tambaye ta ko an biya kudin fansa kafin a sako Omoru, Opalola tace ba a yi mata karin bayani kan lamarin ba.