By Abbas Yakubu Yaura
Wani tsohon kwamishinan lafiya a jihar Legas, Dakta Jide Idris, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jahohi dasu magance matsalolin dake haddasa rugujewar kwakwalwa a kasar nan.
Idris ya yi wannan roko ne a yayin wani taron kimiyya wanda kungiyar Likitoci ta shirya a Legas mai taken: “Kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya a Legas.”
Idris ya ce, aikin dan Adam na da matukar muhimmanci ga ci gaban jihar, inda yace hakan ne ya sanya ake samun ci gaba a fannin kiwon lafiya.
A cewarsa, zubar da kwakwalwar bata musamman ce ga Legas da Najeriya ba, amma lamari ne daya shafi duniya baki daya.
Sannan ya lura da cewa wannan lamari ya dade yana faruwa a harkar lafiya.
Sai dai yace a shekarun baya-bayan nan ta dauki wani kaso mai tsoka, musamman a Afirka.
Domin magance kalubalen dake tattare da zubar da kwakwalwa, Idris ya shawarci gwamnati data inganta albashin ma’aikatan lafiya da saka hannun jari a fannin.
Kazalika Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Idris ya lura cewa ya kamata a inganta tsarin ilimi da kuma kayan aiki da suka tsufa don biyan bukatun al’umma da kuma dacewa da yanayin duniya.
Dangane da fatansa na shekarar 2022 a fannin kiwon lafiya, Idris ya shawarci gwamnati da ta kara yin hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu ta hanyar shigar dasu tare da inganta fasahar.
Har ila yau, Dr Oluwajimi Sodipo, shugaban kungiyar likitocin, ya bayyana cewa, taken taron na da nufin yin nazari kan kalubalen da ma’aikata ke fuskanta, da kuma hanyoyin da za a bi wajen rike ma’aikatan lafiya, a yayin da suke neman zuwa wasu kasashe daga Najeriya.