By Abbas Yakubu Yaura
Ministar bada agajin gaggawa da kula da bala’oi da cigaban Jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana alhinin ta dangane da gobarar da ta auku a ranar Lahadin data gabata a babban kantin sayar da kayayyaki na Next Cash and Carry dake Abuja.
Inda tace an yi asarar kayayyaki da kadarori na biliyoyin Naira a gobarar.
Mataimakiyar ministar ta musamman kan harkokin yada labarai, Misis Nneka Anibeze ce jiya, a Abuja, ta rawaito cewa Sadiya Farouq ta yi tir da yadda bala’in gobara ke kara ta’azzara a kasar, duk da cewa ta yi kira da a yi taka-tsan- don kaucewa sake aukuwar hakan anan gaba .
“Wannan abin bakin ciki ne dake faruwa a ranar biki.Abin takaici ne ga wadanda suka yi hasarar kayansu da rayuwarsu a wannan mawuyacin lokaci.
“Wannan shine lokacin sanyi kuma yana iya fuskantar tartsatsi da bala’o’in tashin gobara.
“Muna kira ga masu shaguna da ’yan kasuwa da su kara taka tsan-tsan tare da kokarin kashe duk wata na’ura kafin su bar shaguna da kasuwanni.
“Gobarar da ta tashi a Next Cash and Carry abin takaici ne sosai kuma muna addu’ar kada hakan ya sake faruwa anan gaba,” in ji ta.
An sanar da cewa gobarar da ta tashi a harabar kasuwar wanda ta taso ne sakamakon matsalar wutar lantarki.