Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance cikin shiri don yakar ‘yan bindiga da ke addabar al’umma.
A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Talata, Masari ya shaida wa mazauna yankuna, da su yi iyakacin kokarinsu don kare unguwarsu daga hare-hare.
Ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a dawo da ayyukan sadarwa a wuraren da abin ya shafa.
A kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta dage haramcin da ta sanya wa kananan hukumomi 10 daga cikin 17 na jihar.
Masari ya yaba da kokarin jami’an tsaro da kungiyoyin sa-kai da ke yaki da barayin daji
Gwaman ya shawarci mazauna yankin da su tallafa wa jami’an da bayanai kan masu aikata laifuka kan lokaci domin magance matsalar.
“Dole ne mu shirya yin yaki a matsayin daidaikun mutane; a yaki ‘yan fashin domin su miyagu ne kuma suna wakiltar mugaye.”
“Da yardar Allah ba za mu mika kasar nan ga shugabanni masu zuwa a karkashin wannan yanayin ba. Dole ne mu dawo da al’amuran yau da kullun, “in ji shi.