A ranar Talatar da ta gabata ce aka samu tashin tashina a kasuwar Mandate dake garin Ilorin tsakanin wani mai siyar da raken, da mai saye kan N50.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya shafi kowa da ke kasuwar, saboda makaman da bangarorin biyu dake adawa da juna suka fito dashi domin gwamza fada .Wanda kuma Hakan ne ya sanya aka rufe kasuwar na tsawon sa’o’i da dama.
An kuma bayyana cewa an garzaya da wasu mutanen da suka samu raunuka zuwa babban asibitin da ke kusa da yankin.
Sai dai wani labarin ya ce wasu bata gari da suka saba yin kisa a kasuwar sun fara fafatawa da daya daga cikin wadanda abin ya shafa wanda ya kai ga barkewar fadan.
An dakatar da harkokin kasuwanci yayin da rikicin ya ci tura, inda Kuma jami’an ‘yan sandan suka isa kasuwar domin tabbatar da cewa komai ya dai daita.
‘Yan kasuwan a kasuwar, sun bayyana fargabar wani harin da za a iya kaiwa idan har ba a magance matsalar ba.
A lokacin da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya ziyarci wurin, ya ga yadda aka girke ‘yan sanda da wasu jami’an Civil Defence a bakin kofa shiga kasuwar domin dakile tabarbarewar doka da oda.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, Babawale Afolabi, ya ce an samu matsalar ce a lokacin da aka ce wani mutum ya sayi raken Naira 50, amma ya Ji Babu Zaki kwata-kwata.
Ya ce mai siyar da raken ya ki amincewa da bukatar mutumin na canza masa raken, wanda daga baya ya daba wa mai siyan wuka.