Hedikwatar tsaro ta yi gargadi kan sanya kakin sojoji da kayan ado don yakin neman zabe na wasu ‘yan siyasa da wasu mutane marasa izini suke yi.
Mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro, Air Commodore Wap Maigida ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Maigida ya ce an baje hotunan yakin neman zaben wasu gwamnoni sanye da kakin soja, a wuraren da aka sani a jihohinsu.
Ya ce a fili wannan matakin ya sabawa doka kuma cin zarafi ne na baiwa fararen hula damar sanya kakin soji a lokacin atisayen soja.
A cewarsa, ya zama dole a sake bayyana cewa rundunar sojin Najeriya a matsayinta na kwararrun hukuma, ta ci gaba da kasancewa a siyasance, don haka ba za ta so a jawo ta cikin kowace irin salon siyasa ba.
“Saboda haka, yana da muhimmanci a shawarci ‘yan siyasa da sauran su, su daina amfani da kakin soji da kayyayakin al’amuran siyasa da sauran taruka daga yanzu.
“Don Allah a lura, duk wanda aka samu da laifi a wannan batun zai fuskanci hukunci,” in ji shi. (NAN)