By Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar masu samar da ruwan leda reshen jihar Kogi ta sanar da karin farashin ruwan leda da aka fi sani da “Pure Water” daga Naira 10 zuwa N20.
Masu samar da ruwan leda sun danganta matakin nasu da tsadar kayan da ake samu sakamakon canjin Naira zuwa Dala.
Jaridar Aminiya ta gano cewa kungiyar ta kara girman adadin buhun ledar ‘pure water’ a shekarar da ta gabata daga naira 100 zuwa naira 130 sakamakon abin da ATWAP ke kira da tasirin tattalin arzikin da annobar cutar COVID-19 ta fara yi.
Shugaban kungiyar, Mista Joseph Eseyin ya sanar da haka a wata tattaunawa da manema labarai a Lokoja, babban birnin jihar a ranar Laraba.
Ya ce yanzu za a siyar da buhun ruwan leda kan Naira 200 saboda halin da ake ciki na tattalin arziki.
Ya kara da cewa, matakin ba wai yana nufin kawo wa masu amfani da ruwan wahala ba ne, illa dai don rage illar tsadar kayayyaki da ake samu da kuma baiwa ‘yan kungiyar damar samar da ruwan sha wanda ya dace da tsarin hukumar kula da magunguna ta kasa.
Eseyin ya kara da cewa litar man fetur ya karu zuwa N165 yayin da na fina-finai da buhuna a yanzu sun haura naira miliyan 1.6m kan kowace tan da kuma naira 7000 kan ko wane damfi, ciki har da farashin dizal.
Sannan Ya ce da sabon farashin buhun ruwan pure water zai zama naira 20 a fadin jihar ta Kogi. Eseyin ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa dasu ba kungiyar hadin kai a sabon tsarin farashin.
Eseyin ya jaddada cewa ATWAP na shirin gudanar da atisayen tsaftar muhalli na kwanaki 3 domin ba su damar samar da isassun tsari a kasa domin yiwa masu amfani da shi hidima a jihar.