Gwamnonin jam’iyyar PDP na can a gidan gwamnatin jihar Rivers dake Fatakwal domin yin wani taro.
Gwamnonin jihohin Enugu, Abia, Benue, Oyo, Bauchi da Adamawa da kuma mataimakin gwamnan jihar Zamfara sun isa Rivers ranar Lahadi.
Yayin da ya zuwa yau gwamnonin jihohin Bayelsa da Taraba su ma suka iso.
Ba a fayyace makasudin taron ba amma akwai rade-radin cewa tattaunawar za ta ta’allaka ne kan makomar jam’iyyar PDP gabanin babban zaben 2023.