By Abbas Yakubu Yaura
Uwargidan shugaban kasa, Misis Aisha Buhari, a ranar Litinin, ta karbi bakuncin mataimakiyar shugabar kasar Laberiya, Dakta Jewel Howard-Taylor, da tawagarta, da wasu shugabannin mata na jam’iyyar APC a ofishinta.
An shirya taron ne gabanin taron mata masu ci gaba na kasa wanda zai gudana a Abuja ranar Talata (yau).