Ministan Sadarwa da bunkasa tattalin Arziki na zamani, Dr Isa Patanmi, ya ce za a shirya cibiyar tattara bayanai na gwamnatin tarayya a jihar Kano nan da sanyya wato rabin-rabi na farkon shekarar 2022.
Patanmi, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake duba cibiyar a ranar Asabar din da ta gabata a Kano, ya ce cibiyar tana da karfin ma’adana terabyte 41, yayin da ma’aunin ta ya kai kusan 2.2.
Ya ce kamfanin na Galaxy ne ke gudanar da aikin a karkashin kulawar ma’aikatarsa.
Ministan ya bayyana cewa, an gina cibiyar ne domin samar da karin wuraren ajiya ga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu a kasar.
“Na zo nan ne don duba aikin, in duba ingancinsa da kuma takamaiman bayanin da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi a baya da dan kwangilar don tabbatar da daidaito.
“Na yaba da ingancin aikin da ake yi a nan, samar da wutar lantarki da kuma tsaron yankin.
“Gwamnati tana da babbar cibiyar tattara bayanai a Abuja, wata kuma a Kudu, wacce ake ajiyewa, wannan kuma wata ce a Arewa maso Yamma.
“Abin da ya fi muhimmanci shi ne, na Abuja da kuma wadda aka kafa wasu shekaru da suka wuce. Amma wannan cibiya a nan ta fi girma saboda ita ce cibiyar bayanai ta mataki na hudu.
“Wanda muke da shi a Abuja ita ce cibiyar data tier three wato ta tattara bayanai na uku. Don haka, wannan shi ne inganta cibiyoyin bayanai da muke da su a kasar nan,” inji shi.
A cewar dan kwangilar ya shaida masa cewa, cibiyar za ta fara aiki a watan Fabrairu, yayin da sauran gine-gine kamar ofisoshi, za su kasance a shirye a watan Maris.
“Shirinmu shine mu tabbatar da cewa nan da rabin-rabi na farko na shekarar 2022, wannan aikin zai kasance a shirye domin kaddamar da shi,” in ji shi.(NAN)