By Abbas Yakubu Yaura
Sama da gawarwaki 400 ne suka kone a wata gobara da ta tashi a dakin ajiye gawa na babban asibitin Onitsha a jihar Anambra.
Gobarar wacce ta dauki kimanin sa’o’i uku a ranar Asabar, ta kone ginin dakin ajiye gawa da ke bayan ginin asibitin.An ce gobarar ta tashi ne daga wani daji da ke bayan dakin ajiye gawarwakin.
Wata majiya ta shaidawa Jaridar Dimokuradiyya cewa a lokacin da gobarar ta tashi, ma’aikatan gawarwakin sun zuba ruwa domin kashe wutar.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa da gobarar ta yi kamari, sai suka kira hukumar kashe gobara ta jihar.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci wurin a ranar Lahadin da ta gabata, abin ya tayar da hankali sosai, domin iyalan da suka ajiye gawarwaki a dakin ajiyar gawa sun koka da yadda lamarin ya faru.
Wasu da suka zo daukar gawarwakinsu domin binnewa, sai suka fashe da kuka a lokacin da suka ga dakin gawarwakin ya ruguje.
Daya daga cikinsu mai suna Charles Ozor ya ce, “Mun zo ne mu dauki gawar wani dan unguwar domin mu binne gawarwakin sai mukaga gawarwakin da ke dakin ajiye gawarwakin sun kone ba tare da an gane su ba. Mun rude; ba mu san abin da za mu yi ba.”
Wani ganau da bai so a bayyana sunan sa ba, ya cewa wani ne ya share dajin da ke bayan dakin ajiye gawarwaki ya banka masa wuta.
Ya ce, “Dajin ya dan yi nisa da dakin ajiyar gawa. Amma kafin mu san abin da ke faruwa, sai muka ga rufin dakin ajiye gawarwaki ya kama wuta. Akwai gawarwaki sama da 400 a cikin ginin. Wuta ta cinye gaba dayan wurin. Kafin ma’aikatan kashe gobara su zo, gobarar ta yi barna sosai; akasarin gawarwakin sun kone kurmus, wasu kuma ba a gane su ba.
“Jami’an kashe gobara sun yi ta fafatawa don hana gobarar tashi zuwa wasu gine-gine. Hasali ma ruwan da ke cikin tankinsu ya kare; sai da suka je suka sake cika tankin a wani wuri domin asibitin ba shi da wurin ruwa a harabarsa.”
Wata ma’aikaciyar agaji da bata so a ambaci sunanta ba, ta shaida wa Jaridar PUNCH cewa an ba da kwangilar dakin ajiyar gawar ga wani ma’aikaci mai zaman kansa.
Ma’aikacin dakin ajiye gawa, wanda ya bayyana sunan sa da Emma, ya ce, “Na je Awka ne domin in kawo gawarwaki. Ina nan sai aka sanar da ni labarin gobarar a waya, sai na garzaya zuwa wajen. Kafin in iso nan, gobarar ta yi barna sosai.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Anambra, Mista Martin Agbili, wanda ya tabbatar da cewa gobarar ta tashi ne daga dajin da ke kusa da wajen ya kara da cewa jami’an kashe gobara sun fafata don hana wutar bazuwa zuwa gine-ginen da ke kewaye.
Ya ce, “Mun samu kiran gaggawa daga babban asibitin Onitsha, kuma mun tura jami’an mu da kayan aikin kashe gobara domin kashe gobarar.