Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Kasa JAMB ta sanar da ranar da za a fara jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta 2022 da kuma jarrabawar shiga kai tsaye, ta DE.
Daraktan hulda da jama’a na hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, a cikin sanarwar hukumar na mako-mako.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa bisa ga sanarwar, aikin rajistar zai fara ne a watan Fabrairu 2022.
Hukumar ta ce za a fara rajistar UTME/DE daga ranar 12 ga watan Fabrairu, 2022, kuma za ta kare a ranar 19 ga Maris.