By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya nuna alhinin sa bisa rasuwar tsohuwar sakatariyar gwamnatin jihar Legas, Princess Adenrele Adeniran-Ogunsanya, wadda ta rasu a ranar Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.
Adeniran-Ogunsanya, wanda ta rasu tana da shekaru 74 a duniya, kafin rasuwarta ta kasance tsohuwar SSG ta jihar Legas a wa’adin farko na mulkin tsohon Gwamna Babatunde Fashola tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamna Sanwo-Olu, Mista Gboyega Akosile, a ranar Talata, yace gwamnan ya jajanta bisa rasuwar tsohuwar SSG, inda ya bayyana cewa mutuwarta babban rashi ne ga jihar.
Sanwo-Olu ya ce, “A madadin gwamnati da jama’ar jihar Legas, ina so in mika sakon ta’aziyyata ga ‘yan uwa da abokan arziki da abokan siyasar marigayiya sakatariyar gwamnatin jihar Legas (SSG), princess Adenrele Adeniran – Ogunsanya.
“Mutuwar princess Adenrele Adeniran-Ogunsanya babban rashi ne ga jihar Legas. Ta yi tasiri wajen bada gudummawa da yawa a lokacin rayuwarta don ci gaban jihar Legas a matsayin sakatariyar gwamnatin jihar Legas Ta kuma yi tasiri sosai a siyasar Legas a lokacin da take jam’iyya mai mulki musamman a Ikko.
“Ina addu’ar Allah ya baiwa princess Adenrele Adeniran-Ogunsanya hutawa na har abada, ya kuma baiwa iyalai, da abokan arziki, abokan siyasa da mutanen Ikorodu kwarin guiwar jure wannan rashi mara misaltuwa.”
Comments 1