Super Eagles zata dawo da ƙarfin ta — Iwobi ya bada tabbaci
Ɗan wasan Ƙungiyar Super Eagles Alex Iwobi ya bayyana godiyar sa ga saƙon fatan Alkhairi ga magoya bayan Ƙungiyar, kwanaki biyu bayan ƙungiyar, ta rasa wasan ta ga Tunisia, a kashi na biyu, wanda yayi sanadiyar fitar ta a gasar wasan ta na AFCON na Shekarar 2022.
A rubutun daya wallafa a shafin sa na Twitter a ranar Talata, Everton Winger ya godema magoya bayan Ƙungiyar ya bayyana cewar, Ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafar zata dawo da karfin ta domin yiwa ƙasar yaƙi.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanwo-olu Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan Tsohuwar SSG Adeniran-Ogunsanya Inda Yace Babban Rashi Ne Ga Legas
“Abun farin ciki, zai iya zama na baƙin ciki. Idan har ta ɓangaren wasan ƙwallon ƙafa ne, magoya bayan mu, sun cancanta muyi wasa domin birge su,” Iwobi ya bayyana a Twitter.