Tsohon Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Hamman Bello Ahmad Kojoli, ya rasu yana da shekaru 73 a duniya.
Wani dan uwasa Mai suna Dokta Umar Ardo ne, ya tabbatar da cewa Kojoli ya rasu ne da yammacin jiya a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.
“Gaskiya ne ɗan’uwanmu ya rasu. A yanzu haka muna kan hanyarmu ta zuwa babban Masallacin kasa domin yin shirye shiryen yima Sallar jana’iza” inji shi.