Tunda rade-radi ya fara yawo akan cire tallafin mai, sai ‘yan kasuwa da kuma ‘yan ina da bala’i suka fara kokarin ganin sun rufe gidajen mai, domin talakka ya shiga wahala.
Wasu kuma suka canja farashi yayi gaba domin kawai su su walala shikau tallakka yayi duk yadda zaiyi.
Inaganin dama akwai alaka da wadanda suka fitar da rade-radin da kuma mugayen ‘Yan kasuwa masu so mu fada a dogon layi da kuma tsadar mai a wannan kasa.
Dama can suna so su samu damar da zasu Dora riba amma basu samu ba, sai yanzu da aka samu Wannan barakar Ita kuma Gwamnati ta yi Uf da Bakinta.
Ya kamata gwamnati tayi magana ga ‘Yan kasuwarnan matukar sunaso su fita daga zargin ‘yan Nijeriya akan ganin zasu iya kara kudin mai ko a a.