Hukumar Kula da Kafafen Yaɗa Labaru ta Kasa, ta dakatar da shirin nan da ake gudanarwa a gidan rediyo Vision FM, Idon Mikiya na tsawon watanni shida.
An kuma ci gidan Talabijin tarar Naira Miliyan 5.
Wannnan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na Hukumar BBC Balarabe Shehu Ilelah ya sanyawa hannu, tare da tura shi ga Manaja-Darakta na Vision.
Takardar tace dakatar da haska shirin ya fara ne daga 28 ga watan Janairun Shekarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: An harbe tsohon dan takarar wata Karamar hukuma a Kaduna, da abokinsa a Abuja
Dakatarwar, a cewar takardar, ya biyo bayan dubi da NBC tayi akan shirin a ranar 5 ga watan Janairun a gidan rediyo na Vision FM da gidan talabijin na Farin Wata TV.
“Tattaunawar ku akan wasu al’amura ciki harda naɗa Shugaban Hukumar Kula da bayanan sirri ta Ƙasa (NIA), ya saɓa da dokar sashe na 39(3)(b) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda ya sanya doka akan hana tattaunawa akan abubuwan da suka shafi Hukumomin tsaro ko hukumomi.
“Haska shirin dake fallasa sirri da sauran al’amura da suka shafi ƙasa shiyasa ya saɓawa dokar.
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Manaja-Darakta na Vision FM Shu’aibu Mungadi ya tabbatar da karɓar takardar, yace kamfanin bai saɓa da dokar da aka sanya na tsayar da shirin.
Amma ya bayyana cewar “idan ka karanta dokar da akace an saɓa, zaku ga cewa ba’a saɓa dokar da NBC tace an saɓa ba.
Akan kuɗin da aka ci su tara, Mungadi yace “bana tunanin zamu biya tarar da’ita kan ta, sabo da shirin Idon Mikiya shirine dake janyo masu sanya tallata suna sanyawa, ana sa kuɗi a shirin, idan ka dakatar dashi, ka tsayar da wuraren da kuɗin ke samu.