Wakilinmu Shu’aibu Ibrahim Gusau
Hukumar Hisba ta Kasa Reshen jihar zamfara, karkashin jagorancin Dr. Atiku Balarabe, ta bukaci duk wata mace wadda iyayenta suka ki daura mata aure da wanda take so, to ta garzayo hukumar hisba a share mata hawaye.
Hakan ya fitone daga bakin shugaban hukumar ta Hisba ta jihar zamfara, Dr Atiku a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa dake Gusau Babban Birnin jihar, yace baiwa iyaye dama su daurawa yarinya Aure wata damace suka samu daga Allah.
Yace iyaye su daina kin daurawa yara mata aure da wadanda suke so, matukar dai ba da wani hakki ba na Shari’a, Ya ce iyaye suna iya nunawa yarinya illolin da suka gani daga wanda yarinyar take so, su kuma bata shawarwari.
Sai Dai shugaban ya bukaci su kuma yaran kada su ci mutuncin iyayensu, idan basuda hujja na kin yarda da wanda iyayensu suka basu, Ya ce domin yanzu ba’a sure dole, Ya Kara da crew duk Wanda iyaye suka yarda da mutuncinshi da addininshi aka basu to su yarda su Karba.
Shehin malamin Ya ce saudayawa idan ba’a baiwa budurwa wanda take so ba, shi saurayin yana daukan kudi ne ya baiwa budurwan domin su hadu a wani gari Daban, don haka ya bukaci iyayen yara dasu rika kaucewa jefa su yaran cikin halin lalacewa.
Dr Atiku ya bukaci duk wata yarinya Budurwa ko Bazawara wadda iyayenta Suka ki bata Wanda takeso to tazo hukumar ta hisba a daura masu aure, amma Ya ce kada yarinya ta yarda wani masoyinta ya dauki kudi ya bata domin ta gudu tabar gidansu domin ya kai ta wani gari.
Shugaban yace wannan masoyin nata zai jefata ne cikin wani mawuyacin hali na bata mata rayuwa kawai, domin a cewarshi matukar shi wannan saurayin nata ya batata zai ajiyetane kawai ba zata sake ganin shi ba domin bukatar shi ta biya.