Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka birnin Addis Ababa domin halartar taro na 35 na kungiyar Tarayyar Afirka a kasar Habasha.
Kwana hudu ake sa ran Buhari zai yi a kasar ta Ethiopia yayin wannan ziyara kamar yadda kakakinsa Malam Garba Shehu ya tabbatarwa da manema labarai.
A lokacin wannan ziyara shugaba Buhari zai hadu da sauran shugabannin kasashen nahiyar inda za su tattauna kan batutuwan da suka shafi neman mashala ga matsalolin da suka danganci siyasa, tattalin arziki da sauran larorin da ke addabar nahiyar.
Haka kuma Buhari zai halarci tarukan kulla hulda da wasu shugabanni a gefen taron, musamman kan yadda za a yaukaka harkokin cinikayya, tsaro da samar da ci gaba mai dorewa.