Jami’an Rundunar Ƴan Sandan Jahar Lagos sun gano wata Mota ƙirar Lexus ES 330 da aka sace a wurin ajiye Mota na Illasan akan hanyar Lekki-Eppi tare da kama wani Mumuni dake da hannu a satar Motar.
A sace motar da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Asabar 29 ga watan Janairun, kuma duk wani ƙoƙarin gano ta, ba’a samu nasara ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Ce Najeriya Za Ta Cigaba Da Neman Zaman Lafiya Da Cigaban Nahiyar Afrika
Rahoton Ƴan sanda akan lamarin ya nuna cewa ƴan sanda dake aiki a Ikorodu sun gano motar kwana ɗaya bayan gudanar da bincike.
Tace “an gano ta garejin Igbogbo na Ikorodu. An kama wani da ake zargi a dalilin satar motar, kuma a halin yanzu yana taimakawa ƴan sanda da bayanai.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewar wanda ake zargin ya nuna cewa bai san an sace motar ba.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar CSP Adekunle Ajisebutu ya bayyana cewar Kwamishinan Ƴan sanda Abiodun Alabi ya bada umarnin ayi bincike akan lamarin.