Shugaban kasa Muhammadu Buhari ranar Asabar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya ce Najeriya za ta ci gaba da neman zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka, da ma sauran sassan duniya, ta hanyar ci gaba da kokarin tabbatar da adalci, daidaito da kuma hada kai a harkokin duniya.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina.
Shugaba Buhari a ganawarsa da firaministan kasar Falasdinu, Mohammad Shtayyeh, a tarukan kungiyar tarayyar Afrika da ke gudana a gefe, ya ce kasar na ci gaba da jajircewa wajen tallafawa dimokuradiyya, da ci gaba, da shugabanci na gari, musamman wajen tabbatar da hakkokin daidaikun mutane da hukumomi.
“A matsayinmu na kasa, muna yin iya kokarinmu, kuma za mu ci gaba da yin iya kokarinmu don tabbatar da adalci da daidato,” in ji shi.
Shugaban ya tabbatar wa shugaban na Falasdinawa cewa Najeriya za ta kasance “daidai” wajen samar da zaman lafiya da ci gaba, tare da kiyaye ka’idojin adalci.
A nasa jawabin, shugaban na Falasdinu ya bayyana cewa, al’amura a yankin gabas ta tsakiya musamman dangantakarsu da Isra’ila sun tabarbare cikin shekaru da dama, yana mai cewa akwai bukatar duniya ta san gaskiyar lamarin.
Shtayyeh ya godewa shugaba Buhari bisa rawar da yake takawa a nahiyar.
“Mai girma Shugaban Kasa, mun gode maka da hikimarka. Muna buƙatar ƙari yanzu. Da fatan za a ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya, domin muna bukatar hikimar ku,” inji shi.
Comments 1