By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane biyu ne aka rawaito an kashe a wata arangama da ‘yan kungiyar asiri suka yi a unguwar Agbarho da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.
An ce lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi.
A lokacin da aka tuntubi shugaban kungiyar cigaban Agbarho-Urhobo, Cif Monday Igho-Odiphri, ya tabbatar da mutuwar mutane da ba a san adadinsu ba a lamarin.
Ya kuma tabbatar da cewa an shawo kan lamarin yayin da jami’an tsaro, ciki har da ‘yan banga na yankin suka yi kasa a gwiwa don kamo masu laifin.
Ya kuma kara da cewa lamarin bai da alaka da kone-kone da aka kai a fadar masarautar Osuivie na masarautar Agbarho a makon jiya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Bright Edafe, ba’a samu damar jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, saboda wayar sa a kashe.