Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa guda 52 a ranar Lahadi a Abuja tayi kira ga mazauna Jahohin Sokoto, Zamfara da Katsina da kuma Jahar Niger dake fama da matsalar tsaro da su kare kawunan su akan ƴan ta’adda wanda ka iya kawo hari, ko kuma sanya haraji a garesu.
Ƙungiyar wanda ta bayyana cewa adadin ƴan Arewa guda 500 da aka kashe a sati huɗu, ta kuma bayyana cewa akwai kuma rahotannin kashe-kashe, da sace-sace da cin mutunci da yawaitar makamai a Jahohin guda huɗu.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Shiga Jimamin Rasuwar Shahararriyar Mai Waka Ta Kasar Indiya Lata Mangeshkar
Shugaban Ƙungiyar ta CNG Balarabe Rufa’i wanda ya bayyana haka a taron Manema labaru bayan taron ta, domin yin dubi akan yanayin tsaro a Arewa, yace yanzu lokaci ne daya kamata su kare kawunan su akan ƴan ta’adda.
Yace ” Gamayyar Ƙungiyoyin Arewa ta kuma yi dubi akan kai hare-hare a faɗin Jahohin Arewa a kwanakin da suka gabata a matsayin abun damuwa.
“Mun damu sosai akan kashe mana mutane, da lalata rayuwar mu, ta hanyar fyaɗe, da cin mutuncin mata da talauci a kauyuka daga ƴan ta’adda.