Kungiyar dalibai (SUG) ta Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso, ta jagoranci yin Wani gagarumin zanga-zangar adawa da matakin da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya dauka na yunkurin sauya sunan jami’ar.
Shugaban SUG, Anuoluwa Adeboye, da jami’in hulda da jama’a, na kungiyar Gabriel Michael, a wata budaddiyar wasika da suka raba wa manema labarai a ranar Juma’a, sun ce canza sunan makarantar zai yi illa ga martabarta.
Jaridar Daily Trust a ranar Asabar din da ta gabata ta ruwaito cewa gwamnan ya aikewa majalisar dokokin jihar kudirin canza sunan jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola (LAUTECH) zuwa jami’ar Ladoke Akintola da ke Ogbomoso (LAU).
Sai dai kungiyar ta ce sauya sunan jami’ar zai yi mummunan tasiri ga martabanta, tana mai cewa karfin da aka riga aka samu da sunan makarantar duk za a iya mantawa da shi.
Ta bukaci gwamnan da ya duba ciki ya yi la’akari da shawarwari masu kyau kan yadda cibiyar za ta ci gaba
Comments 1