By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sabunta tashar duba sakamako (IReV) don tabbatar da ingantaccen aiki.
Sanarwar da kwamishinan na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye ya fitar ta ce, “An yi hijirar (URL) daga www.inecelectionresults.com zuwa www.inecelectionresults.ng.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Duk takardun shaidar mai amfani da aka yi wa rajista daga tsohon URL ɗin suna nan akan wannan sabon URL ɗin.
Sannan yace “Za a aika da saƙon imel ɗin da ke ɗauke da sabon URL ga duk masu amfani da rajistar.
“An ɗora sanarwar hakan zuwa dandalin sada zumunta na Hukumar.”