Matashi Mai Bada Taimakon Jin Kai Abubakar Shehu Kaikai Ya Gwangwaje Yan Asalin Karamar Hukumar Kusada Mazauna Abuja Da Kyautar Keke Nafef Da Mashina
Matashin Dan Siyasa Kuma Mai Bada Taimakon Jin Kai Injiniya Abubakar Shehu Kaikai, ya bayar da Kyautar Motar Kurkura da Mashina ga Yan Asalin Karamar Hukumar Kusada Mazauna Kubwa,Birnin Tarayya Abuja.
Matashin Injiniya Kaikai ya bayar da Kyautar ne bayan kokenda Yan Asalin Karamar Hukumar Kusadar suka yi mashi na taimaka masu domin neman abinci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar PDP Ta Akwa Ibom Bata Rabuba Kan Amincewa Da Dan Takarar Gwamna – Emmanuel
Matasan dai sun mika koken ne a sa’ilinda ya ziyarce su domin yin zumunci da kuma duba halinda suke ciki a harkokin su na yau da kullum.
Kamar yadda matasan suka bayyana,babu wani dan siyasa ko mai hannu da shuni dan Shiyyar Daura da ya taba ziyartarsu don ganin halinda suke ciki sai a wannan karon da Injiniya Kaikai ya ziyarce su.
Sun bayyana farin cikinsu akan wannan tallafi da Injiniya Abubakar Shehu Kaikai ya basu sai suka yi addu’a akan Allah SWT ya kara albarka ga dukiyar shi.
Sun kara da cewar, suna sane da irin ayyukan jin kan al’umma da yake gudanarwa a yankuna da dama na Karamar Hukumar Kusada.
Daga nan sai suka roke shi akan ya dubi girman Allah SWT ya nemi kujerar siyasa domin su maida biki akan tallafinda ya yi masu.
Masu magana da yawun matasan daga nan suka yi kira ga Yan Asalin Yankin nasu masu hannu da shuni da suke zaune a Abuja akan su yi koyi da Injiniya Abubakar Shehu Kaikai domin Allah SWT ya sanya albarka a dukiyar su.
Da yake maida jawabi, Injiniya Kaikai ya nanata kudirinshi na cigaba da tallafawa mabukata domin su san cewar al’umma ta kula da su.