By Abbas Yakubu Yaura
Mutane biyu ne ake fargabar sun mutu a wani hatsarin mota daya rutsa dasu a hanyar Mbima-Yenagoa a jihar Ribas a ranar Asabar.
Wani ganau mai suna Fyneface ya ce hatsarin ya rutsa da wata babbar mota mallakar wani kamfanin gine-gine da wasu motoci uku.
Ya yi ikirarin cewa ya ga gawarwaki da sauran wadanda suka jikkata da aka ciro daga cikin motocin.
“Ina dawowa daga tafiya sai motar da nake ciki ta zo wurin. Har muka sauka don jin abin da ya faru.
“Daga abin da na tattara, motar ta fito ne daga Yenagoa, jihar Bayelsa, lokacin da ta yi karo da sauran motocin,” in ji ganau din.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya reshen jihar Ribas Salisu Galadunchi yace har yanzu bai samu rahoton lamarin ba.
Ya ce, “Ba zan ce hakan bai faru ba, amma ba a kai rahoto ga FRSC ba.
“Tunda lamarin ya shafi mutuwa, mai yiwuwa mutanen da abin ya shafa sun je wurin ‘yan sanda.
“Na kuma nemi jami’ai na da su tabbatar ko ‘yan sanda suna sane don mu sanya shi a cikin bayananmu.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton hadarin ba.
Sai dai ta yi alƙawarin mayar da martani da zarar ta samu karin bayani. Inda har yanzu Iringe-Koko ba tayi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.